Babu Abin Da Na Fi So Kamar Faranta Ran Marayu Da Raunana – Adesuwa Udo

MADAM ADESUWA OGECHI UDO, matashiya ce wadda ta tashi cikin maraici da rashin gata, amma hakan bai hana ta samun yin karatu har zuwa matakin Jami’a ba. Sannan ta yi gwagwarmaya a vangarori iri dabandaban, wanda ya kai tag a zama shahararriyar ‘yar fim na Hausa da kuma Turanci. Bugu da qari kuma, a halin yanzu ita ce Shugabar Gidauniyar ‘Empowerment Foundation (ELS)’, wacce har Masallaci ta gina tare da tallafawa marasa galihu ba tare da nuna banbancin addini ko qabila ba, duk kuwa da kasancewar ta na kirista wadda ba musulma ba. Ta samu kyatuka da lambar yabo a qashashen Turai kamar Ingila da Amurka da kuma nan gida Nijeriya. Wakilinmu MUSTPHA IBRAHIM KANO, ya samu zantawa da ita kamar haka:

TATTAUNAWA


Za mu so mu jin cikakken sunanki da taqaitaccen tarihinki a taqaice? Sunana ADESUWA OGECHI UDO, an haife ni a Kano amma iyayena mutanen Jihar Benin ne, na yi makarantar Firamare a kwakwaci daga nan na wuce Sakandire ta Xanware duk a nan Kano, daga nan...

Read latest Leadership Hausa online.

Online newspapers at PressDisplay. Newspapers from Nigeria
Newspapers in Hausa